Siyasa

Malam Sha’aban Sharada ya sha alwashin sanya karatun kur’ani ya zama tilas a dukkan makarantun jihar Kano

Spread the love

Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar ADP, Sha’aban Sharada, ya ce zai kafa cibiyar binciken Alkur’ani idan aka zabe shi, inda ya sha alwashin sanya karatun kur’ani ya zama tilas a makarantu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin majalisar yakin neman zabensa, Abbas Yusha’u ya fitar a ranar Lahadi.

Mista Sharada ya bayyana hakan ne a lokacin da yake sanar da malaman addinin Musulunci na Kano shawararsa ta tsayawa takarar gwamna. Ya ce yana da matukar muhimmanci a gana da su domin malamai su ne masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da tunanin al’ummar Kano.

Ya gabatar da kudirin doka a majalisar wakilai na kafa cibiyar binciken alkur’ani ta kasa a Kano.

Dan takarar gwamnan, kuma dan majalissa mai wakiltar mazabar karamar hukumar birnin Kano, ya ce za a gudanar da karatun farko da na biyu na samar da cibiyar a cikin mako mai zuwa.

Mista Sharada ya sanar da malamai cewa cibiyar binciken kur’ani mai tsarki na koyar da ilimin kur’ani za ta kasance a Kano, ganin yadda jihar ke da rinjaye a wajen masu haddar alkur’ani a Najeriya.

Dan majalisar ya bayyana cewa, idan aka zabe shi gwamna, zai wajabta karatun kur’ani a makarantun firamare da na gaba da firamare na Kano, ya kuma bukaci malamai da su zama makasudin aiwatar da manufofi da tsare-tsare na gwamnati.

Dan takarar gwamnan ya yabawa limaman da suka amsa gayyatar kuma ya ce a matsayinsa na shugaban al’umma zai ci gaba da ganawa da su kan muhimman batutuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button