Siyasa

Matashin Ɗan Siyasa Daya Fice Daga APC Saboda Tsadar Kuɗin Fim Nasu ya koma Jam’iyyar YPP ya Sayo Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa.

Spread the love

Adamu Garba idan za’a iya tunawa , a kwanakin baya ya nemi tallafin yan Najeriya domin siyan fom ɗin takarar shugaban ƙasa, biyo bayan ayyana ₦100,000,000 da APC suka ayyana nasu.

Cikin ikon Allah, saboda tausayin ƴan Najeriya suka tattara masa kuɗi kimanin miliyoyin nairori, amma ya ɗinke kuɗin sa ya canja jam’iyya.

A yau ta tabbata, matashin ya sayo fom. Duk da bai faɗi adadin kuɗin fom ɗin ba, amma duk da haka alama na nuna cewa Adamu Garba zai cika burin sa na ganin ya zama shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar YPP.

A kwanakin baya Adamu Garba, ya ce game da kudin da aka tara masa yanzu ya ce duk wanda ke son kudinsa to ya sanar zai turawa mutum kudinsa.

Wannan ne dai karo na biyu da ya nemi takarar shugaban ƙasa bayan yunƙurinsa na 2019, ba tare da ya sayi fom ba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button