Siyasa

Matsala ta kunno kai yayin da kotu ta yankewa shugaban jam’iyyar APC hukuncin zaman gidan yari a jihar Kano

Spread the love

Kotun majistare ta yanke wa shugaban jam’iyyar APC mai mulki a gundumar Yautar jihar Kano hukunci bisa laifin mallakar katinan zabe sama da 300 ba bisa ka’ida ba.

Faroukh Ibrahim Umar wanda ya jagoranci kotun ya yankewa Aminu Ali hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin mallakar katin zabe na dindindin guda 367 ba bisa ka’ida ba.

An tattaro cewa an kama Ali ne a watan Oktoba da laifin karbar katin zabe daga mutane daban-daban a karamar hukumar Gabasawa ta jihar Kano. An kuma zarge shi da hada baki da wasu ‘yan jam’iyya mai mulki domin aikata laifin, kuma ya amsa laifinsa. Wani mataki da ya saba wa sashe na 22 (a) na dokar zabe, 2022 kamar yadda aka gyara.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun ya yi fatali da zabin biyan tarar N500,000 na laifin farko. Kotun ta kuma yanke wa Ali hukuncin daurin watanni shida tare da biyan tarar Naira 50,000 bisa laifin hada baki, wanda ya saba wa sashi na 97 na kundin laifuffuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button