Matsalar Tsaro: Gwamnoni Sun Gana da Sufetan Yan Sanda a Abuja

Shugaban ƙungiyar gwamnoni NGF kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi tare da takwaransa na jihar Kebbi, Mr. Abubakar Bagudu, sun gana da muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa ranar Talata.

Gwamnonin sun yi wannan ganawa ne da IGP domin tattaunawa kan hanyoyin da gwamnonin zasu taimakawa hukumar yan sanda ta daƙile ƙalubalen tsaron da ake fama dashi, kamar yadda Thisdaylive ta ruwaito.

A yayin taron nasu, muƙaddashin sufetan yan sanda, Usman Alƙali Baba, yace da haɗin kan gwamnonin “Yan sanda zasu magance abinda ake ganin bazai magantu ba’.

Gwamnonin sun bayyana cewa sun kawo ziyara hedkwatar yan sandan ne domin su taya sabon sufetan murnar shiga wannan babban ofis.

Sannan kuma su jajanta masa bisa hare-haren da aka kaima wasu jami’an yan sanda a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Fayemi yace:

“Mun kawo wannan ziyara ne domin mu taya sabon sufeta murna, Kuma hukumar yan sanda tana da babbar rawa da zata iya taka mana a matsayin mu na gwamnoni, waɗannan sune dalilan mu na kawo wannan ziyarar.”

“Bayan taya sufeta murna, muna kuma yi masa jaje da ta’aziyya bisa rashin wasu jami’an yan sanda a wannan yanayi da muke ciki na ƙalubalen tsaro da yaƙi ci yaƙi cinyewa a ƙasar nan.”

“Waɗannan sune jarumai na gaske, waɗanda suka bada rayuwarsu don su kare tamu, saboda haka munzo nan a madadin gwamnoni mu mika ta’aziyyarmu ga IG, sannan mu tattauna kan yadda za’a magance faruwar haka nan gaba.”

Shugaban gwamnonin ya kara da cewa, gwamnoni sun bada gudummuwarsu kuma zasu cigaba da taimakawa hukumar yan sanda ta ɓangarori da dama da suka haɗa da; Kuɗi, kayan aiki da kuma wasu shirye-shirye.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *