Miyagu na shirin fito da wasu bidiyoyin karya domin ci mani mutunci – “Inji – Pantami”

Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa akwai wani tuggun da ake yunkurin shirya masa.

Jaridar Punch ta ce Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 26 ga watan Afrilu, 2021, ta bakin hadimarsa, Uwa Suleiman.

Mai taimaka wa Ministan wajen yada labarai, Uwa Suleiman, ta fitar da jawabi, ta na bayanin makarkashiya na gaba da aka shirya wa mai gidanta.

A cewar Ministan, yanzu abin da ya rage shi ne a fito da bidiyoyi na karya da aka hada domin a cin ma burin da ake da shi na ganin an goga masa kashi.

Ga abin da jawabin ya ce:

“Mu na da ingantaccen bayanan sirri cewa wasu da su ke ta fadi-tashi, su na yaki da Pantami, za su koma wa makarkashiya na gaba a wannan aikin na su.”

“Wannan karo, miyagun su na neman wadanda za su yi masa dako, su fito da bidiyoyin bogi da za su nuna Ministan a wani irin yanayi domin bata masa suna.”

“Sam ba mu yi mamakin wannan sabon shiri ba, wanda ya nuna yadda su ka dage da karfi da yaji bayan a baya sun gaza samun nasarar ci wa Ministan mutunci.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *