Mun Yi Nasarar kama Mutane 2 Cikin Wadanda Suka Kashe Hausawa 2 a Jihar Ribas, Inji ‘Yan Sanda.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ribas ta ce ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a harin na ranar Lahadi a kan al’ummar Hausawa a karamar Hukumar Oyigbo da ke jihar ribas.

Idan Baku manta ba a ranar Asabar, rikici ya barke tsakanin Ibo da Hausawa yayin da Hausawa biyu suka mutu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr. Joseph Mukan, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba ta hannun mai magana da yawun rundunar, Nnamdi Omoni, ya kara da cewa an tura wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar.

Mukan ya ce, “Kwamishinan‘ yan sanda ya kira bangarorin sannan ya kulla yarjejeniya. An binne gawarwakin Hausawan biyu da suka rasa ransu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

An yi wa yankin kawanya tare da karfafa tsaro a yankin Inji Sanarwar. ”

Ya tabbatar wa dukkan mazauna Oyigbo cewa su kare lafiyarsu kuma ya gaya masu cewa su ci gaba da gudanar da ayyukansu na halal ba tare da jin tsoron komai ba.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.