Na Fara Addu’a Allah Ya Tsige Shugaba Buhari Daga Mulki, in ji Fasto Wale Oke

Wani fasto a jihar Ibadan ya bayyana cewa, yana mai addu’ar Allah ya tsige shugaba Buhari.

Faston ya bayyana haka ne duba da yadda kasar ke fuskantar matsaloli ta kowace fuska a yanzu.

Hakazalika ya ce shi ba ya tsoron wani abu ya faru dashi, saboda haka ba ya tsoron harin makiya Shugaban kungiyar Pentikostal Fellowship of Nigeria (PFN), Bishop Francis Wale Oke, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza matuka a mulkinsa, The Nation ta ruwaito.

Ya ce ya fara addu’ar Allah ya tsige shugaba Buhari don Najeriya ta dandana zaman lafiya. Ya siffanta gazawar gwamnatin Buhari da yawaitar zub da jini da kawanyan da ake ta yi wa kasar.

Ya ce ko a lokacin yakin basasa, Najeriya ba ta ga kashe-kashe da yawa ba, yana mai cewa sabanin lokacin da yankin Gabas kadai ke tafasa, a yanzu dukkan sassan kasar na fama da hare-hare.

Oke, wanda kuma shi ne Bishop na The Sword of the Spirit Ministries dake Ibadan, ya yi kira da a tsige Shugaban idan hakan zai samar da hanyar zaman lafiya da ake so a kasar.

Ya yi magana ne a babban dakin taro na Jami’ar Precious Cornerstone (PCU), Garden of Victory dake jihar Ibadan.

Ya ce: “A cikin shekarun 1960 lokacin da Najeriya ta yi yakin basasa, yankin gabashin kasar shi ne fagen yaki.

“Abun bakin ciki a yau, ko ina a Najeriya fagen yaki ne inda ake kashe-kashe da zubar da jini a kasar a kowace rana.”

Ya kara da cewa abin kunya ne yadda gwamnati ba ta iya yin komai ba lokacin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye jami’a mai zaman kanta ta Greenfield da ke Kaduna suka sace dalibai.

A cewarsa: “Wasu mugaye sun yi awon gaba da wasu daliban inda suka nemi a ba su N800m don a sake su; sun kashe wasu.

“Gwamnati ba ta iya daga dan yatsa ba kuna gaya min cewa Shugaban kasa bai gaza ba? Buhari ya gaza! ” “A karon farko, na tsinci kaina ina addu’ar Allah ya tsige Buhari.

Sun sace dalibai ba tare da gwamnati ta yi komai ba kuma kuna gaya min cewa gwamnati ba ta gaza ba? “Shin cewa kuke ba za mu iya tunkarar gwamnatin da ba ta iya aiki ba wacce kayan aikinta suka durkushe?” Ya kara da cewa: “Bana jin tsoron kowa.

Ba ni bane! Ni dan aiken Madaukaki ne, Yana kula da ni. Babu harsashin makiya da zai kashe ni; Mutuwa ta ba za ta zama a hannun mutum ba.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *