Siyasa

Na ki amincewa da tayin tikitin takarar Sanata da Tinubu yayi min – Wike

Spread the love

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Juma’a, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress, Bola Tinubu, ya zaburar da shi ya koma jam’iyya mai mulki da tikitin takarar Sanata.

Ya ce tsohon gwamnan jihar Legas ya ba shi tikitin takarar ne bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kasa cika alkawari bayan ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

Sai dai ya ce ya ki amincewa da wannan tayin tare da dagewa cewa zai ci gaba da zama a babbar jam’iyyar adawa duk da korafin da ya ke yi, inda ya ce bai taba tsayawa takara a zaben fidda gwani na takarar mataimakin shugaban kasa ko na sanata ba.

“Ban yi takara ba don haka ba zan zama dan takarar mataimakin shugaban kasa, ni ba kamar sauran da ba su da kima suka sayi fom din Sanata tare da fom din shugaban kasa bane, shi ya sa lokacin da Tinubu ya ba ni takarar majalisar dattawa, ban je ba. Wike ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ke gudana a Fatakwal.

A ranar 8 ga watan Yulin 2022 ne jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wasu gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar APC sun gana da Wike a Porth Harcourt, babban birnin jihar Rivers gabanin zaben 2023.

Gwamnonin sun hada da Kayode Fayemi; Rotimi Akeredolu da Babajide Sanwo-Olu na jihohin Ekiti, Ondo, da Legas bi da bi.

Sauran a cikin tawagarsu sun hada da zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji; tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Ayodele Fayose, da dai sauransu.

Kafin ziyarar gwamnonin APC, an samu rahotannin cewa dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da Wike sun gana a kasar Faransa. Sai dai kuma mai taimaka wa tsohon gwamnan jihar Legas kan harkokin yada labarai Tunde Rahman ne ya karyata rahotannin, wanda ya bayyana su a matsayin “labari na karya”.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa watakila gwamnonin APC sun yi kaca-kaca da Wike da shugabancin PDP bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar adawa na shugaban kasa don jan hankalin gwamnan Ribas a bangaren su gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button