Na Yarda Kwankwaso ya cancanta ya zama shugaban Kasa domin ya taimaki rayuwar Al’umma kuma yayi aiki da yawa ba kamar Atiku ba ~Cewar kashim Shettima.

Dan takarar Neman mataimakin Shugaban kasar Nageriya a karkashin jam’iyar Apc Sanata kashim Shettima ya bayyana hakan a wata firar tattaunawar Kai tsaye da sukayi a shafin yanar gizo wanda suka gudanar tare da Dan Jarida Jaafar Jaafar da Barista bulama da Kuma Abba Hikima
Shettima Yana Mai cewa Ba zan iya furta wa kwankwaso wata Kalmar zagi ba domin ya yi wa jihar Kano aiki da yawa a zahiri.
Ya taimaki mutane da yawa amma ga wasu waɗanda suka riƙe matsayin mataimakin Shugaban kasa ba za su iya ƙidaya aƙalla mutane uku ba wanda suka taimaki rayuwarsu ba ko Kuma don ka zuba jari a masana’antun giya ba tsakani da Allah Kwankwaso ya cancanta inji Sen kashim shettima.
Sanata Shettima Yasha yabon Kwankwaso Kuma yasha bayyanawa duniya cewa Kwankwaso Shugaban al’umma ne na gari