Nayi imani cewar, Bola Ahmed Tinubu ƙiris ya rage yakai shekara ɗari ba sittin da tara ba kamar yadda yake amfani dasu — Femi Fani Kayode.

Tsohon ministan tarayyar Nijeriya, mutumin nan mai yawan yin zantuka masu kawo kace-nace, Femi Fani Kayode ya furta wata magana wacce ta girgiza mutane kuma ta yamutsa hazo tamkar aradu zata faɗo akan jigo a jam’iyyar APC kuma uba ga jam’iyyar, wato Bola Ahmed Tinubu.

FFK

A wani saƙo daya aike ta ƙafar sadarwar sa ta dandalin Facebook, FFK ya faɗawa dubban mabiyansa cewa, Tinubu ya doshi shekaru ɗari, bawai shekaru 69 da shugaban yace sune shekarun sa ba.

Daga nan ne, FFK ya shawarci duk wani mutum aƙili kuma mai basira, da yayi watsi da duk wani zance da zai ƙara fitowa daga bakin Tinubu, na cewa wai shekarun sa sittin da tara.

Ga rubutun FFK ɗin da yayi:

Kamar yadda aka gani daga sama, abine da yake a bayyane cewa:

“idan wani ya faɗa maka cewa mutumin da yake a cikin hoton nan shekararsa 69, ka faɗa masa cewar ni, FFK nace ƙarya yakeyi. Jemagen da ake gani, shekarunsa sun doshi ɗari, bawai 69 ba.”

Tinubu

Abune mai kyau a tuna da cewa, a kwanakin baya ne Tinubu ya yamutsa hazo da zancen shekarunsa, inda wasu suka dinga cewa ai shekarun da yake amfani dasu sunfi adadin shekarun sa na zahiri, inda kuma wasu suke cewa, ai wannan ba komai bane face irin abin nan da ƴan Hausa ke kira na yarfen siyasa, duba da shekarar 2023 ta zaɓe tana ƙara ƙaratowa, wanda ana sa ran Tinubun yana cikin yan gaba gaba na waɗanda ake tunanin zasu iya gadar kujerar mai girma shugaba Muhammadu Buhari.

Koma dai menene, lokaci ne zai nuna.

Menene ra’ayin akan wannan batu? Bayyana ra’ayinka.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *