Siyasa

Nayi matukar murna da farin ciki da haryanzu Kwankwaso yana cikin jam’iyarmu ta PDP ~Cewar Bukola Saraki.

Spread the love

Tsohon Gwamnan jihar kwara Kuma tsohon shugaban majalisar dattijan Nageriya Abubakar Bukola saraki ya bayyana farin cikinsa tare da jin dadin da cewa haryanzu tsohon Gwamnan Jihar kano Eng Sanata Rabi’u musa kwankwaso haryanzu Yana cikin jam’iyarsu ta PDP Saraki ya Fadi hakan ne a shafin sa na Facebook Yana Mai cewa Na yi murna kasantuwar abokina Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu shi ɗan Jam’iyyar PDP ne. Lallai ya yi abin da ya dace.

Na tattauna da wasu cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga Kano – waɗanda suka kawo min ziyara makon da ya gabata a gidana dake Abuja, ina da ƙarfin gwiwa cewa Sanata Kwankwaso da tawagarsa za su ci gaba da zama cikin jam’iyyar don mu gina tare da ceto Nijeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button