
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, (rtd) ya ce idan aka kwatanta da yadda ake cin hanci da rashawa a Najeriya, sun kasance waliyai a zamanin mulkinsa na soja.
Babangida ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust da a ranar Lahadi.
Ya ce, “Na kori wani gwamna ne saboda karkatar da N300,000. Yanzu akwai mutane – muna karantawa a cikin jaridu da shafukan sada zumunta da sauransu – suna sace Naira biliyan 2, biliyan 3 kuma ba wanda ya ce sun yi almundahana; mu kawai saboda mu sojoji ne, shi ke nan.
“Har yanzu ina tabbatar da cewa mu waliyai ne idan ka kwatanta wanda ake zargi da satar Naira biliyan 3 da naira 300,000; to ina ganin mu waliyyai ne”.
Game da dalilin da ya sa yaƙi da cin hanci da rashawa ke da wuya, ya ce: “Ina da wani ra’ayi amma saboda ya fito daga gare ni, ba wanda yake so, ba wanda zai so ya ji ta:
“Gano wuraren cin hanci da rashawa da kai musu hari daga tushe. Na karanta a daya daga cikin jaridu inda alkali ke korafin cewa ba a biyansu albashi mai kyau a wurin jama’a kuma hakan tabbataccen tushe ne na cin hanci da rashawa.
“Duk inda ka ke da tsarin da ka ke da iko da yawa za a samu cin hanci da rashawa.