Siyasa
PDP ce za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023 – Atiku ya tabbatar

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa, Atiku Abubakar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa, kasancewar daya daga cikin tsofaffin jam’iyyun siyasar kasar, za ta lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2023. .
Atiku ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kaddamar da wani ofishin yakin neman zabe a jihar Gombe a ranar Asabar.
Ofishin yakin neman zaben da ke a kan titin Bauchi Road, Gombe, zai kasance wani dandali na inganta manufofin siyasa na dukkan masu rike da mukamai na jam’iyyar PDP a babban zabe mai zuwa.
Dan takarar shugaban kasa tare da tawagarsa sun tafi Abuja kai tsaye bayan kaddamar da ofishin yakin neman zaben.