Siyasa

PDP za ta dakatar da yakin neman zabe a Imo kan harin da aka kai gidan dan takararta

Spread the love

An zargi ‘yan bindiga da kone-kone sun kai farmaki gidan Mista Ugochinyere, inda suka kashe mutane hudu ciki har da kawunsa.

Jam’iyyar PDP a Imo ta ce za ta dakatar da yakin neman zabenta kan harin da aka kai gidan Ikenga Ugochinyere, dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar Ideato North/South.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce za a dakatar da yakin neman zaben na tsawon mako guda, inda ta kuma ce jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zanga-zangar nuna adawa da harin da aka kai a mahaifar dan takarar a Akokwa.

An yi zargin cewa a ranar Asabar din da ta gabata ce, wasu motoci dauke da ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan Mista Ugochinyere, inda suka kashe mutane hudu ciki har da kawunsa.

Mista Ugochinyere kuma shi ne mai magana da yawun gamayyar jam’iyyun siyasa.

Sanarwar ta PDP ta ce za a gudanar da zanga-zangar adawa da kisan ne a ranar Laraba da karfe 10:00 na safe kuma ta yi kira ga ‘yan takarar zabe da su zo da shugabanni 10 daga kowace karamar hukuma.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button