RAM MAZA YA BACE/ Tsaron kasa: Buhari ya fusata, yace Ortom baya ganin laifin kansa, na wasu yake hange

Fada shugaban kasa tace Buhari ya matukar fusata da kalaman Gwamna Samuel Ortom – Buhari yace dama laifi ai tudu ne, Samuel Ortom yana take nasa inda yake hango na wasu.

Gwamna Ortom ya zargi Buhari da goyawa Fulani baya a kasar nan inda suke cin karensu babu babbaka Fadar shugaban kasa tayi martani kan zargin da gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya jefi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shi a kan matsalar tsaro.

Ortom a ranar Talata ya zargi shugaban kasa Buhari da yi wa Fulani aiki domin su karbe Najeriya a martanin da yayi kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa wanda ake zargin makiyaya ne.

Amma kuma mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, Malam Garbe Shehu, ya kushe ikirarin Gwamna Ortom.

A wata takarda mai take ‘Gwamna ortom matsalar wasu kawai yake hangowa, bayan hangen tasa,’ wacce Shehu ya fitar a ranar Alhamis, ya ce shugaban kasa ya matukar damuwa da kashe-kashen da ake yi tare da ikirarin gwamnan.

Ya ce, “Shugaban kasa ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda aka rasa a kashe-kashen kwanan nan a jihar Binuwai.

“Bugu da kari, yace karuwar miyagun al’amuran ballantana kashe-kashe da fada a yankunan kasar nan yana bukatar hadin kan dukkan hukumomin tsaro domin hana cigaban faruwar lamurran.

“Ya kara da bayyana fushinsa tare da kunyar da kalaman Samuel Ortom, Gwamnan jihar Binuwai suka bashi inda ya zargi shugaban kasan da gwamnatinsa bayan mummunan abinda ya faru a jiharsa.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *