Sa’insa Ta Barke Tsakanin Jam’iyyar PDP Da APC A Jihar Edo Biyo Bayan Harbe-Harbe Da Ya Faru A Jihar.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ke zargin APC da yi wa jam’iyyar su zagon kasa lokacin gangamin yakin neman zaben ta, itama jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP da hayo wasu lalatattun matasa wanda su ka yayyaga fastocin dan takarar jam’iyyar ta su.

Takaddamar ta barke ne Biyo bayan harbe-harbe da ya faru a ranar Asabar 13 ga watan Ogustan shekarar da muke ciki, yayin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar adawa ta PDP, dake gudana a Apanam a karamar hukumar Etsako dake yammacin jihar Edo, Lamarin da ya sanya jam’iyyar PDP ke zargin jam’iyyar APC da hanata rawar gaban hantsi.

Wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP dake karamar hukumar da lamarin ya faru, mai suna Imonofi Osumah, ya zargi cewa, wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon kwamishina Lucky James shine wanda suke kalubalanta da kitsa harin.

Rahotanni sun bayyana cewa, Yayin harbe-harben mutane uku sun samu raunuka kamar yadda jarida Punch ta rawaito.

Da yake mayar da martani sakataran yada labarai na jam’iyyar Chris Azebamwan, ya nisanta jam’iyyar APC da cewa, Sam bata da Hannu a lamarin da ya faru.

Haka zalika ya zargi jam’iyyar PDP da hayo ‘yan daba, inda suka zargi cewa sun lalata fastocin dan takarar jam’iyyar tasu Pastor Osagie Ize-Iyamu.

Shima a tabakin Dan takarar jam’iyyar APC Pastor Osagie Ize-Iyamu ya bayyana cewa jam’iyyar su ta gudanar da dukkan gan gaminta cikin lumana a dukan fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.