Sakamakon rikicin cikin gida jam’iyar APC ta dare gida biyu a jihar Kano

Sabon Rikici Ya ƙara Ɓallewa A Jam’iyar APC Ta Dare Gida Biyu A Jihar Kano

Jagoran magoya bayan shugaba Buhari a ƙarƙashin inuwar jam’iyar APC Abdul Majid Ɗanbilki wanda aka fi sani da ‘Kwamanda’ ya ayyana sabuwar ƙungiya a cikin jam’iyar APC wacce za a ƙaddamar nan da ƴan kwanaki masu zuwa mai laƙabin ‘APC Aƙida’

Ɗanbilki ya bayyanawa manema labarai a ranar Talata daya ke maida martani dangane da dakatar da shi da aka yi daga jam’iyar APC da hukumomin jihar su ka yi

Ya bayyana cewa wannan darewar da jam’iyar ta yi gida shine ra’ayin wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyar

“Batun dakatar da ni daga jam’iyar APC, ba a bi hanyoyin da suka kamata ba kuma babu wani kwamitin bincike da aka kafa ko kuma wani gargaɗi da aka gindaya mini, kawai dai an bayyana an dakatar da ni ne babu wata hujja” in ji Ɗanbilki Kwamanda.

“Kuma wannan hukuncin zai taɓa martabar jam’iyar a jiha sannan shugabannin da suka zartar da wannan hukuncin za su yi nadama daga baya ko da sun ɗauki matakin ne domin su tsorata wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyar da suka zaɓi Sanata Barau Jibril a matsayin ɗan takarar gwamnansu na gobe”

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *