Siyasa

Sama da N400m Aka tara Domin Gina Sakatariyar APC ta Katsina

Spread the love

Magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne suka tara zunzurutun kudi har naira miliyan 470 domin gina babban sakatariyar jam’iyyar a jihar Katsina.

An bayar da wadannan gudummawar ne a ranar Asabar a yayin kaddamar da asusun roko na gina katafaren ginin da aka gina a titin Hassan Usman Katsina, a karamar hukumar Batagarawa.

Babban mai ƙaddamar wa Architect Kabir Ibrahim Faskari wanda aka fi sani da “Kebram” ya bayar da kaso mafi tsoka a cikin kudi Naira miliyan hamsin (₦50,000,000) yayin da hamshakin dan kasuwar Katsina Dahiru Bara’u Mangal ya bayar da Naira miliyan talatin (₦30,000000).

Sauran wadanda suka bayar da tallafin sun hada da gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari; Mataimakin sa Mannir Yakubu; Kakakin majalisar dokokin jihar Hon Tasi’u Maigari Zango da kuma gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle wanda ya bayar da gudunmawar kudi har miliyan uku da miliyan biyu da miliyan biyar da kuma Naira miliyan daya.

Wasu daga cikin bakin jihar Legas da Katsina da suka hada da kwamishinoni da masu ba gwamna shawara na musamman Aminu Masari suma sun bayar da gudunmawar da suka kai miliyan ashirin, miliyan sha bakwai, miliyan goma, miliyan biyar, miliyan biyu, miliyan daya, dubu dari biyar, naira dubu dari daya, da Naira dubu hamsin.

Gwamna Aminu Masari da yake jawabi jim kadan bayan bayar da tallafin ya ce ana sa ran kammala ginin nan da watanni hudu masu zuwa.

Ya bayyana fatan cewa idan aka kammala za a kaddamar da tsarin rantsar da sabon dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a ranar 29 ga Mayu, 2023.

“Akwai gudummawa da dama da wasu mutane da dama suka bayar ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran wadanda ba sa son a bayyana sunayensu saboda dalilai na siyasa.

Masari ya ce, “Daga kallon abubuwa, kudaden da aka samu zuwa yanzu za su ishe mu don samun wani ci gaba ko kuma kammala dukkan aikin.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button