Sanata Uba sani ya tallafawa ‘yan kasuwar jihar Kaduna da ku’di Naira Milyan Ashirin 20m domin samun damar mallakar shaguna a sabuwar kasuwar zamani.

Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar APC Sanata Uba sani ya tallafawa Yan kasuwar jihar Kaduna da ku’di har naira Milyan Ashirin Sanatan ne ya bayyana hakan da kansa a shafinsa na Twitter Yana Mai cewa a Kokarin da na ke cigaba dayi neman gidan Kashim Ibrahim na samu gagarumin ci gaba a yau yayin da kungiyar ‘yan kasuwan Arewa tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Kaduna daga dukkanin kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar suka bayyana baki daya suka nuna goyon bayansu ga takarara ta da Kuma takarar dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed. Tinubu da jam’iyyar APC a jihar Kaduna.

A lokacin da nake jawabina a wajen taron, na gode wa kungiyar da suka taru domin bayyana goyon bayansu ga takarara da jam’iyyar APC a jihar Kaduna. Na tabo kokarina a matsayina na Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya kuma a matsayina na Shugaban Banki kwamitin Bankuna, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi inda ya bani dama na taimaka wa al’ummai ta hanyar Babban Bankin CBN wajen taimaka wa gidaje sama da 12,000 ta Shirin Nan na SMEs da tallafi da lamuni don bunkasa sana’o’insu sakamakon annobar COVID-19 bisa la’akari da Matsin akan tattalin arziki.

Domin samun ci gaba da kokarin gwamnatin jihar da ta riga ta gina manyan kasuwanni na zamani, na tallafa wa ’yan kasuwa masu tasowa da kudi Naira Miliyan Ashirin (N20,000,000) wanda zai taimaka musu wajen samun kashi 10% na hannun jari don mallakar shaguna. a kasuwanni a fadin jihar. A yayin da nake tabbatar musu da kudurin da nake da shi na karfafa kokarin gwamnati mai ci na bunkasa tattalin arzikin jiharmu mai albarka, na yi alkawarin ci gaba da samar da rance mai sauki don taimaka wa ‘yan kasuwa masu bukatar jarin kasuwanci.

Masu jawabai daban-daban sun yi ta bi-da-bi-da domin bayyana shirinsu na tafiya da ke gaba wajen tabbatar da nasarar babbar jam’iyyarmu. Na kuma bi sauran jami’an jam’iyyar wajen karbar dubunnan ’yan takarar jam’iyyar PDP zuwa babbar jam’iyyar mu ta All Progressives Congress (APC).

Amatsayin Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna na jam’iyar APC Sanata Uba sani na cigaba da samun karbuwa a idon Al’ummar jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *