Siyasa

Sati Mai Zuwa Kwankwaso Zai Miƙa Bukatar sa ta Neman Takarar Shugaban Ƙasa a Hukumance.

Spread the love
Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso

A sati Mai zuwa ne idan Allah ya kaimu ake kyautata zaton cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro na ƙasa Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso Zai bayyana gamida miƙa buƙatar sa ta tsaya wa takarar shugaban ƙasa s ƙarƙashin tutar jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Da yake zantawa ga manema labarai a ranar juma’a data gabata, Kwankwaso yace, sai da ya gama tuntuɓar ko wani lungu da saƙo na ƙasar nan kafin yanke wannan hukunci, kuma sakamakon tuntuɓar ya nuna akwai alamun nasara.

A cewar sa:

“Na yi ta tuntuɓar abokai da ƴan Nijeriya masu sha’awa daban-daban kuma sakamakon ya kasance mai kyau. Zan sanar da ƴan Najeriya burina na siyasa a farkon mako mai zuwa,” inji shi.

Tsohon gwamnan ya ce goyon bayan jam’iyyar NNPP ya yi matukar bada mamaki dangane da nasarar da aka samu a gangamin rajistar mambobinta da aka kammala kwanan nan.

Ya ci gaba da cewa zaɓen shekarar 2023 zai kasance ne tsakanin masu son kawo sauyi a al’amuran Najeriya da kuma masu son ci gaba da riƙe matsayinsu na masu juya tattalin arzikin ƙasa.

Kwankwaso ya kuma yi kira ga gwamnatoci da jami’an tsaro da su kara kaimi wajen magance matsalar rashin tsaro, yana mai cewa akwai bukatar gwamnati ta karfafa karfin jami’an tsaro na murkushe ‘yan ta’adda.

Ya ce a matsayinsa na tsohon ministan tsaro bai taɓa tunanin rashin tsaro zai ƙara ta’azzara ba har ya zuwa yanzu. Saboda haka ne yasa Kwankwaso ya ce, dole ne shugabancin ƙasa ya zaburar da sojoji, horar da sojoji da kuma horar da sojoji da kuma samar da kayan aikin da ake buƙata waɗanda dole ne su zarce abin da ƴan fashi da ƴan ta’adda ke dasu.

Ya kara da cewa:

“Na yi imanin cewa tsaro yana ɗaya daga cikin ɓangarorin da za mu bawa muhimmanci da nuna ƙwarewa domin ƴan Najeriya su sake samun ƴancin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.”

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button