Saura Kiris ’Yan Boko Haram Su Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, “in ji Gwamnan Neja”

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya ce mayakan Boko Haram sun yi kusa da babban birnin kasar., Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana lokacin da ya ziyarci sansanin ‘Yan Gudun Hijira a ranar Litinin, gwamnan ya ce ‘yan ta’addan sun karbe wani yanki na jihar bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza a kokarin samar da tsaro a jihar.

Ya ce ya tuntubi Gwamnatin Tarayya a lokuta daban-daban amma babu wani abu mai amfani da ya fito daga kokarinsa.

Gwamnan jihar Neja ya bayyana cewa, ‘yan Boko Haram na daf da shiga birnin Abuja idan ba a kula ba – Ya gargadi cewa, tsakanin in da suke yanzu a jihar Neja da Abuja tafiyar awanni biyu ne kacal.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *