Siyasa Ba Gaba Ba: Kwankwaso Ya Ziyarci, Wamako.

Tsohon gwamnan Jihar kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Ziyarci Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakadda Wamako.

Kwankwason ya Ziyarci Wamako Yayi masa jaje kan Rasuwar ‘Yarsa Hajiya Sadiya Wamako da ta rasu Sakamakon Haihuwa.

Kwankwaso ya Jajantawa Wamako Yayi addu’ar Allah ya Jikanta da Rahama yasa ta huta.

Sanata Aliyu magatakadda wamako ya nuna Farinciki da jindadi matuka bisa ziyarar Ta’aziyyar da Tsohon Ministan Tsaron Ya kai masa.

Wamako ya jinjinawa kwankwaso yayi masa fatan Allah ya maidashi Gida Lafiya.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.