Siyasa

Tabbas Yanzu na aminta Shugaba Buhari mutun ne mai Gaskiya kuma na kowa da kowa ~Cewar Bola Tinubu.

Spread the love

Dan takaran Shugaban Ƙasa a Inuwar Jam’iyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya bayyana Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin “Shugaba na gaskiya, Dan-uwa kuma Aboki” wanda ya nuna halin ya kamata, Nutsuwa da korewa” cikin makwanni da aka gudanar da Babban taro na Musamman na Jam’iyar APC.

Cikin sako daya aike ga Shugaban Kasa, wanda shida kansa ya rattabawa hanu, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya nuna godiya cikin wasikar daya aike wa shugaban Ƙasa na taya shi murna, ya kara da cewa yayin da dukkanin Ƴan takarar ke dakon Shugaban Ƙasa ya “zabo guda” dazai gajeshi, cikin ruwan sanyi ya bada dama ga kowa ya taka rawan sa.

Bisa ga Dan takaran yace lallai ka cika cewa “Kai na kowa ne cikin Jam’iya kuma babu wani Dan takara guda da kai nashi ne a Jam’iyan ce”.

Ya taya Shugaban Ƙasa Murna na kammala Babban taron Jam’iyar cikin Nasara ya kuma bashi tabbaci cewa za’a maida hankali kan nuna abinda aka cimma a yayin yaƙin neman zaben gama gari na 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button