Siyasa

Tawagar Gwamna Wike sun sanar da janyewa daga yakin neman zaben Atiku a hukumance

Spread the love

Sansanin gwamna Nyesom Wike na jam’iyyar PDP a hukumance ya sanar da janyewa daga shiga yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

Kungiyar ta bayyana matsayar ta ne bayan wata doguwar ganawa da ta fara da misalin karfe 7 na daren jiya zuwa karfe biyu na safiyar yau a gidan Wike mai zaman kansa da ke Fatakwal babban birnin jihar Ribas.

Mambobin kungiyar sun ce babu daya daga cikinsu da zai shiga ko wace irin matsayi a majalisar yakin neman zaben sai dai idan shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu ya ajiye mukaminsa.

A kwanakin baya ne aka nada wasu ‘ya’yan kungiyar a matsayin shugabanni da mambobin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.

Wadanda suka halarci wannan taro na ma’ana a gidan Wike da ke Fatakwal sun hada da Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo; Tsohon Gwamna Olusegun Mimiko na Ondo, Ayo Fayose na Ekiti, Donald Duke na Cross River, Ibrahim Dankwambo na Gombe da Jonah Jang na Plateau, tsohon Atoni Janar na Tarayya, Mohammed Adoke.

Sauran da suka halarci taron sun hada da dattijan jihohi, Olabode George, Jerry Gana; Shugaban Jam’iyyar PDP na Kudu-maso-Kudu, Dan Orbih; tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Chibudom Nwuche; Sanata Suleiman Nazif, Nnenna Ukeje, da dai sauransu.

Bayan shafe sama da sa’o’i bakwai na ganawar sirri daga karfe 7 na yammacin ranar Talata, 20 ga watan Satumba zuwa karfe 2 na safe ranar Laraba 21 ga watan Satumba, sun hallara don yiwa ‘yan jarida bayani kan sakamakon, inda George ya bayyana ficewar.

Matakin na sansanin gwamnan Ribas ya zo ne kwanaki kadan zuwa ranar 28 ga watan Satumba, ranar da ‘yan takara za su fara yakin neman zabe kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button