Siyasa

Tinubu ya tabbatar mana zai kafa matatar gwal a Zamfara – Gwamna Matawalle

Spread the love

Gwamnan Zamfara ya ce Mista Tinubu da kan sa ya tabbatar masa da shirinsa na “kafa matatar zinare a jihar”.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, ya yi alkawarin kafa matatar zinare a Zamfara idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Asabar.

Mista Matawalle, wanda shi ne kodinetan yakin neman zaben jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma, ya bayyana cewa, Tinubu ya riga ya samar da wani tsari na magance matsalolin tsaro a jihar da ma kasa baki daya.

“Ni da kaina na tambayi dan takarar shugaban kasa ko yaya zai shawo kan matsalar tsaro a jiha ta, ya ce zai kafa matatar zinare a jihar.

“Kafa matatar gwal za ta magance matsalar ‘yan fashi, garkuwa da mutane da sauran laifuffukan da ke cutar da jihar da kuma yankin. Baya ga damar ayyukan yi da samar da arziki a tsakanin al’umma.

“Masu zuba jari za su kuma tallafa wa gine-ginen tsaro na jihar don gudanar da harkokin kasuwancin su cikin sauki,” in ji shi.

Mista Matawalle ya ce tsarin Mista Tinubu yana da wadatar da zai iya tunkarar kalubalen tsaro a Najeriya.

“Muna da kwarin gwiwar cewa shugabancin Tinubu zai samar da taswirar kawar da matsalolin tattalin arziki da siyasa a kasar nan kuma shi kadai ne ke da amsar inganta Najeriya,” in ji shi.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button