Tsarin mulkin dimokiradiyya ba tare da katsewa ba na sama da shekaru 20 ya cancanci yasa a yi murnar samun ‘yanci, in ji Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Kwankwaso ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daura damara kan abubuwan da suke hada kai maimakon raba kasar duk da bambancin al’adu da addinai.

“Bambance-bambancen ban mamaki da yawan abubuwa na Najeriya ta fuskar al’adu, yare, addini da kabilanci na musamman ne, kuma muhimmin karfi da ya kamata ya sanya kowane dan Najeriya alfahari,” in ji Kwankwaso.

Yayi wannan magana ne a Ihitteafor-Ukwu, Imo yayin jana’izar marigayi Augustus Onuoha, mahaifin kodinetan tafiyar Kwankwasiyya na jihar Imo, Collins Onuoha.

Ya ce duk da cewa har yanzu Najeriya na fuskantar matsaloli da dama, amma bai kamata a dauki muhimman nasarorin da aka samu a cikin shekaru 60 da wasa ba.

Tsarin mulkin dimokiradiyya ba tare da katsewa ba sama da shekaru 20 ya cancanci a yi bikin, in ji shi Kwankwaso, amma dole ne a ciyar da shi yayin da kasar ke fara tafiyar shekaru 60 masu zuwa da ma bayanta.

Kwankwaso ya ce ya kasance abokin kawancen Kudu maso Gabas, kamar yadda ya sake nanata kudurinsa na ci gaba da hada kai da Ndigbo don yin aiki da gaskiya wanda zai inganta rayuwar mutanen yankin saboda, a cewarsa, “Lamarin Gabas”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.