Siyasa

Tsawon Shekaru Sha shida PDP tayi tana tarwatsa harkokin Ilimin jihar Kaduna amma yanzu malam El rufa’i ya gyara komai ~Cewar Uba sani

Spread the love

Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Litinin din da ta gabata ya koka da rashin samun ingantaccen ilimi a Kaduna a tsawon shekaru 16 na gwamnatin babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Uba wanda yake amsa tambayoyi daga ‘yan kasuwa da manoma da mata da matasa a wani taron majalisar dattawan yankin kudancin Kaduna da akayi Kafanchan hedikwatar karamar hukumar Jema’a, ya ce gwamnatin PDP na shekaru 16 ta dauki malamai aiki a jihar ta hanyar da ba ta daceba

Uba, wanda ya yabawa Gwamna Nasir el-rufai kan yadda ya canza munanan yanayin ilimi a jihar, ya yi alkawarin karfafa nasarorin da aka samu idan aka zabe shi.

Ya bayyana cewa a lokacin gwamnatin PDP ana daukar malamai ne ta hanyar kason kudi maimakon bin hanyoyin da suka dace don inganta ilimi.

“Na gina katafaren dakin na’ura mai kwakwalwa a Kwalejin Ilimi, Gidan Waya da Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, kafin in yi tunanin zuwa Majalisar Tarayya ko in tsaya takarar Gwamna.

Ya kuma bukaci shugabanni da masu fada aji a kowane mataki da su baiwa hazikan dalibai tallafin karatu, ya kara da cewa bai kamata a bar ilimi ga gwamnati kadai ba.

A cewarsa, ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati mai ci a fannin ilimi, kiwon lafiya, noma, karfafa matasa da mata ya zama wajibi domin tabbatar da samun ci gaba mai dorewa.

“Dukkanmu muna sane da irin sauye-sauyen da ke faruwa a jiharmu mai albarka a karkashin kulawar Malam Elrufai.

“Zan gina kan wadannan tsare-tsare na ci gaba domin kai jiharmu ga wani matsayi mafi girma,” in ji Uba

A cewarsa, ayyukan da suka shafi rayuwar al’umma ne kawai za a baiwa fifiko a gwamnatinsa.

Ya ci gaba da cewa rikom amanar da ya yi a majalisar dattawa ya sa ya samu damar gudanar da mulkin jihar.

“Lokacin da kake neman mukami, yana da muhimmanci ka nuna wa jama’a nasarorin da ka samu a ofishin gwamnati na karshe da ka rike.

“Na dauki nauyin kudirori da yawa kuma na kasance Sanata daya tilo da ya samu kudiri biyu da shugaban kasa ya amince da su.

“Amma ba za a iya cewa haka ba a kan manyan ‘yan takarara na jam’iyyar PDP da Labour Party wadanda su ne ‘yan majalisar dokokin kasar a shekarun baya.

Ya kara da cewa “‘Yan takarar PDP da Labour sun shafe shekaru takwas da shekaru hudu a zauren majalisar ba tare da daukar nauyin wani kudiri ba.”

Dangane da batun tsaro, ya ce dole ne a sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya, a samar da ‘yan sandan Jihohi da baiwa sarakunan gargajiya aikin da kundin tsarin mulki ya tanada, ita ce kadai hanyar da za a magance matsalar rashin tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button