Siyasa

Tun bayan da aka ƙirƙiri Nigeria a alif 1914, ba’a samu nagartacce kuma adalin shugaba kamar Buhari ba. ~Cewar Gwamna Masari

Spread the love

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa tun da aka ƙirƙiri Nigeria a shekarar alif 1914, ba taɓa samun jajirtacce kuma shugaba na ƙwarai kamar Buhari ba.

Masari ya bayyana haka ne a jiya Asabar, yayin da ya halarci wani taro wanda waɗanda suka anfana da shirin NSIP na gwamnatin tarayya suka gudanar a Jihar.

A cewar Gwamna Masari, Shugaba Buhari ya bijiro tare da ɗabbaka tsarin da kowacce gwamnati mai zuwa za ta iya amfani da shi wajen cire ƴan Nigeria daga talauci.

Sakamakon wannan namijin ƙoƙari da aka bijiro da shi, Shugaba Buhari ya cancanci yabo da kuma goyon baya domin cimma babban burin na shirin tallafawa ƴan ƙasa a koda yaushe.

A gefe guda kuma, waɗanda suka amfana da shirin tallafin na gwamnati mai suna NSIP, sun buƙaci Masari ya roƙa musu gwamnatin tarayya domin a sauya shirin ya zama na dindindin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button