Siyasa

Uba sani Yayi Allah wadai da kashe-kashen kananan Hukumomin Giwa Kajuru.

Spread the love

Sanata Uba sani ya ce Labarin kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari da Kajuru abin bakin ciki ne kuma ina tare da Gwamna Nasir El-Rufai wajen mika ta’aziyyata ga wadanda suka rasa ‘yan uwansu a irin wannan mummunan lamari. Haka kuma da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa.

Hare-haren ba gaira ba dalili da barnata rayuka da dukiyoyi abin Allah wadai ne kuma babu wani yunkuri da hukumomin tsaro za su yi face gurfanar da masu laifin gaban shari’a.

Rahoton Daily trust na cewa An kashe mutane 11 a karamar hukumar Giwa, yayin da aka kashe biyu kowanne a kananan hukumomin Kajuru da Birnin Gwari.

Sanata Uba sani shine Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar APC.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button