Siyasa

Wadanda suka lashe mana rumfunan zabe na PDP ne kawai za su samu kwangiloli da mukamai a gwamnatinmu – Atiku

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ‘yan jam’iyyar da ke son samun mukamai da kwangiloli a gwamnatinsa dole ne su tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu nasara a rumfunan zabe.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wani taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Abubakar ya ce jam’iyyar PDP za ta iya lashe zaben shugaban kasa ne kawai idan ‘ya’yan jam’iyyar suka yi aiki domin samun nasarar jam’iyyar a rumfunan zabe daban-daban.

Ya ce shiga cikin jirgin yakin neman zabe na ’yan takara bai isa ya sa su samu mukamai da kwangiloli ba.

“Dukkanku ‘yan PDP ne kuma magoya bayan PDP. Kuna son PDP ta dawo kan mulki, don Allah ina rokon ku, ku tabbatar kun ci rumfunan zabe,” inji shi.

“Kasancewar kana bin dan takarar gwamna ko dan takarar Sanata ko dan takarar majalisar wakilai ko dan takarar shugaban kasa ka yi yakin neman zabe ba shi ne cancantar da za ka samu nadi ba.

“Ba cancanta ba ne za ku sami kwangila ko a matakin kananan hukumomi, jiha ko tarayya.

“Hanya daya tilo, gwargwadon abin da ya shafi ni; idan ni ne shugaban kasa, idan ka zo ka ce kana son aiki ko kuma kwangila kake so, zan ce ka ba ni sakamakon rumfar zabenka, abin da zan ba kowa kenan domin sai dai idan ba mu yi haka ba, ba za mu ci zabe ba.

“Ba za ka iya bin gwamna a ko’ina ba ko sanata a duk wuraren sannan ba ka ci zabe a rumfar zabe ka zo ka ce kana son zama minista ko kuma kana son samun wannan kwangilar.

“Don haka don Allah a matsayinmu na ’yan jam’iyyarmu, mu tabbatar mun koma mazabunmu, mu tabbatar mun kai rumfunan zabe.”

Jigogin jam’iyyar a zauren taron sun hada da Iyorcha Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa; Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa; Namadi Sambo, tsohon mataimakin shugaban kasa; Ademola Adeleke, gwamnan Osun; Aminu Tambuwal, gwamnan Sokoto; da Udom Emmanuel, gwamnan Akwa Ibom.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button