Siyasa
Wanne irin fata kuke ma Nigeria a wasan da zata buga yau da ƙasar Ghana?

Daga | Ya’u Sule Tariwa,
A yau ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nigeria, Super Eagles zata fafata da takwararta Black Stars ta ƙasar Ghana a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya.
A makon jiya ne ƙungiyar ta Super Eagles ta tashi wasa canjaras da ƙasar Ghana, wasan da aka buga a filin Baba Yaro dake birnin Kumasi ta ƙasar Ghana.
Tuni dai shirye-shirye suka kankama na take wasa da misalin ƙarfe 6:00pm na yamma, a filin wasa na Moshood Abiola dake babban birnin tarayya Abuja.
