Siyasa

Wata Sabuwa: Dan Takarar Shugaban kasar Najeriya karkashin Jam’iyar Labour Party Mr Peter Obi ya sami wata Babbar matsala tsakaninsa da Sarakunan Jihohin Inyamurai

Spread the love

Sarakunan Jihohin Inyamurai sun kama dan takarar shugaban kasar Mr Peter Obi da laifin yin Amfani da matasansu wajen tada zaune tsaye a Jihohin Inyamuran da zummar siyasa.

Zuwa yanzu Sarakunan sun bayyana cewa za suyi wani zama na Musamman ijinanunsu don yanke hukuncin karshe game da Takarar ta Mr Peter Obi.

Inda suka bayyana cewa ba zasu taba yarda Mr Peter Obi ya bijiro musu da wata dabi’a da zata iya wargaza tsakanin kawunan matasan su da Dattijan Jihohin Inyamurai ba.

Wanda suka ce tun yanzu ya fara gurbatawa matasan nasu tarbiyya, to ina ga sun sa an zabe shi ya zama shugaban kasar, basu yarda da wannan ba, a cewarsu.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button