Siyasa

WATA SABUWA: Dangwani, Danburam, Dambatta da masu ruwa da tsakin PDP sun zargi Kwankwaso da yin ƙarfa-ƙarfa

Spread the love

Daga | Ahmad Aminu Kado,

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Adamu Yunusa Dangwani, tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Danburam Abubakar Nuhu da Yusuf Bello Dambatta, Kwamishinan Ma’aikatar Ƙasa, sun bi sahun sauran ƴan jam’iyyar PDP a Jihar Kano wajen zargin tsohon Mai gidan su, Sanata Rabi’u Kwankwaso da yin ƙarfa-ƙarfa a jam’iyar.

Dangwani da Danburam da Dambatta jiga-jigan ƴan ɗariƙar Kwankwasiyya ne, kafin a kakar siyasa ta bana su raba gari da jagoran nasu, Rabi’u Musa Kwankwaso.

A wata ganawa da masu ruwa da tsaki na PDP su ka yi a yau Talata, a ofishin tsohon gwamnan Jigawa, Alh. Sule Lamido, sun yi kira ga uwar jam’iya ta ƙasa da ta rushe shugabancin jam’iyar a jihar sabo da yadda ya ke son ya yi ƙarfa-ƙarfa.

A takardar bayan taro da Dambatta, tare da Akilu Sani Indabawa su ka sanya wa hannu kuma a ka taba wa manema labarai, masu ruwa da tsakin sun zargi Kwankwaso da yi wa PDP zagon ƙasa, domin ciyar da jam’iyar da ya ke shirin koma wa, NNPP gaba.

“Yunkurin Rabi’u Kwankwaso na ƙarfa-ƙarfa a Jam’iyyar PDP yayin da a lokaci guda yake gina kishiyar Jam’iyyar PDP wato Jam’iyyar (NNPP).

“Wani salon zagon ƙasa ne Kwankwaso ke yi PDPa Kano inda idan ba a tashi tsaye ba, to za a kai ƙaramin da an hana PDP fitar da ƴan takara a zaɓen 2023 a Kano.

“Akwai lokacin tunda za a rufe siyar da fom din takarar ga ‘yan takara a ranar 1 ga watan afrilu a 2022. Taron ya tabbatar da tsoron shi, domin idan ba a dauki mataki ba PDP zata rasa damar ta na tsayar da dan takara ta barwa NNPP dama.

Taron ya tattauna akan hadin kai da zama tsintsiya madauri daya dan tabbatar da kowa an tafi dashi a tafiyar a yayin sabon shugabancin.

Saboda haka mambobin Jam’iyyar a tsakanin su wanda suka hada da Sule Lamido tsohon gwamnan Jigawa, Aminu Wali Tsohon Minista, Sanata Hayatu Gwarzo, Dakta Akilu Sani Indabawa, Dakta Yunusa Adamu Dangwani da dai sauransu.

“mu na kira ga Kwamitin zartarwa na Ƙoli da ya yi gaggawar rushe shugabancin Kano kuma su naɗa sabon kwamitin riko da zasu gudanar da Al’amuran Jam’iyyar.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Kwankwaso ya ce zai sanar da sauya shekar sa zuwa NNPP ne a karshen watan Maris ɗin nan da mu ke ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button