Siyasa

Wike Ya nada masu bashi shawara guda14,000

Spread the love

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya nada masu ba da shawara 14,000 ga bangarori daban-daban na siyasa a jihar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Kelvin Ebiri ya sanyawa hannu, masu ba da shawara za su taka rawar gani a harkokin gwamnati.

“Baya ga masu ba da shawara 14,000, Gwamna Wike ya kuma nada jami’an hulda da unguwanni 319 da jami’an hulda da kananan hukumomi 40,” in ji Mista Ebiri.

“Nade-naden na nan da nan.”

Ana sa ran Gwamna Wike zai mika mulkin jihar a watan Mayun 2023 bayan wa’adinsa na shekaru takwas ya wuce.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button