Siyasa

Yakamata ace yanzu Gawuna da Garo suna kulle a gidan kurkuku suna fuskantar Shari’a bisa satar kuri’un zaben 2019 ~Cewar Abba Gida-Gida.

Spread the love

Dan takarar ya bayyana hakan ne ta bakin Mai Magana da yawunsa sunusi Bature Yana Mai cewa Kamata ya yi a tuhumi Gawuna da Garo bisa laifukan zabe – Bature yayi martani ga Garba

Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, ta bayyana cewa jam’iyyar APC ta tsayar da dan takarar gwamna da mataimakan gwamna a jihar Kano, ba su da hurumin tsayawa takarar kowane mukami na gwamnati.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sunusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya ce ya kamata a gurfanar da mutanen biyu a gaban kuliya saboda kawo cikas a zaben 2019.

Ya caccaki jam’iyya mai mulki kan yadda ta baiwa Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo tikiti saboda rashin wayewa.

Bature ya ce, maimakon ta sanya musu takunkumi don ba da damar zaben 2019 bai kammalu ba, gwamnatin jihar ta sanya allunan tallata su.

“Abin kunya ne jam’iyyar ta bayar da tikitin ga wadanda faifan bidiyon da suka nuna suna kawo cikas ga zaben da ya bata sunan Kano a duniya.”

Kokarin da ‘yan adawar da a lokacin suke jam’iyyar PDP suka gudanar da wani gagarumin magudi wanda ya sa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ayyana zaben gwamna na 2019 a matsayin wanda ba a kammala ba, ba shi da wata tangarda.

Ya na nan kuma ba za a iya musawa ba cewa a ranar 14 ga watan Fabrairun 2019, rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wasu mutane biyu bayan ta gano buhu 14 dauke da kuri’u da aka buga da babban yatsa domin goyon bayan jam’iyyar APC.

Domin APC ta tuhume mu ko wata jam’iyya da magudi, wauta ce kuma nuna rashin kunya ne ga jama’a, inji shi.

Don haka ya kalubalanci jam’iyyar APC da ta kawo wani lamari na musamman da ‘yan sanda suka kama wani dan jam’iyyar NNPP yana aikata duk wani mataki da ya saba wa ka’idojin zabe. inji Sanusi Bature Dawakin Tofa
Kakakin Dan Takarar Gwamna na NNPP Engr. Abba K. Yusuf

Abba Kabir Yusuf Inkiya Abba Gida-Gida shine Dan takarar neman Gwamnan jihar Kano mafi karfi d a Samun karbuwa ga jama’ar jihar Kano bisa ga bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button