‘Yan bangar siyasa sun kone gidan gwamnan jihar Imo kurmus

Gwamnatin jihar Imo ta sanar da cewa ‘yan ta’adda sun kai hari gidan gwamnan jihar Hope Uzodinma da ke karamar hukumar Omuma Oru ta Gabas.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Declan Emelumba wanda ya tabbatar da labarin, yace an samu jikkata a yayin harin, kafin jami’an tsaro su dakile harin.

Kwamishinan yace an fara binciken musabbabin wannan hari, da ake tunanin ‘yan bangar siyasa ne aka dauki nauyi suka aikata hakan.

Declan Emelumba yace gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su gudanar da bincike domin gano wadanda suka dauki nauyin harin.

Daga; Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *