Siyasa

‘Yan Bindiga Sun Harbi Darakta Matasa Na Yakin Neman Zaben Atiku / Okowa A Jihar Ribas

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, wadanda ake zargin ‘yan bangar siyasa ne, sun harbe darektan kungiyar gangamin matasa na kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa, Mista Rhino Owhorkire na jihar Ribas.

An harbe Owhorkire, wani jigo a jam’iyyar PDP a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida Aluu, karamar hukumar Ikwerre ta jihar a daren ranar Larabar da ta gabata, kuma an garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana ba domin yi masa magani. A cewar wata majiya

Maharan sun fara harbin tayoyin motar Owhorkire kafin su harbe ta a gilashin, daga nan ne harsasan suka taba shi.

Harbin Daraktan Matasan ya faru ne jim kadan bayan wata guda bayan an yi zargin an yi garkuwa da shi tare da tilasta masa yin tir da goyon bayansa ga Atiku.

Majiyar wadda ta yi magana game da yanayin, ta ce Owhorkire yana ya ji rauni, kuma a halin yanzu yana karbar magani a wani wurin jinya da ba a bayyana ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button