‘Yan Kwankwasiyya Ba Kullum Ake Kwana A Gado Ba, Kubar Cika Baki Akan Zaben Ondo, Cewar Alkanawi..

‘Yan Kwankwasiyya Ba Kullum Ake Kwana A Gado Ba, Kubar Cika Baki Akan Zaben Ondo, Cewar Alkanawi..Wani Dan Jarida Mai sharhi akan al’amuran yau da kullum ya shawarci ‘yan Kwankwasiyya da su daina cika baki akan zaben jihar Ondo wanda za a gudanar gobe a Asabar.

Sabiu Alkanawi ya ce a duk lokacin da mutum ya fiya cika baki akan wani abu sai Ubangiji ya barshi da iyawarsa.

Alkanawi ya ce lokacin da ‘yan Kwankwasiyya suka yita cika a zaben fidda gwani na takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP mai gidan su Kwankwaso kwata-kwata kuri’u 58 ya samu a zaben.

Haka zalika lokacin da akayi zaben gwamna a jihar Kano ba bu irin cika bakin ‘yan Kwankwasiyya ba suyi ba suna cewa babu wanda ya isa ya murde musu zabe a Kano, sai gashi rana tsaka anyi wuju-wuju dasu.

Yanzu kuma ganin nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a zaben gwamnan da ya gabata a jihar Edo ne yasa ‘yan Kwankwasiyyar suke ta cika baki akan zaben, shi yasa nake tuna musu da maganar nan ta Malam Bahaushe da yake cewa ba kullum ake Kwana a Gado ba….

Ya kamata ku gane cewa zaben Ondo yana da ban-banci da zaben Edo. A Edo Dan takarar da Kuke goyon baya shine yake Mulki, a Ondo kuwa Dan takarar da kuke so yaci zabe ba shi da mulki, sannan gwamnatin da take da alhakin kula da zaben ba taku bace, dan haka zabe fa sai abin da kuka gani…

Leave a Reply

Your email address will not be published.