Siyasa

YANZU-YANZU: Aminu Minister ya zama shugaban Kungiyar “Za’bin Allah shine za’bin Malam, za’bin Malam shine zabin al-ummar Kaduna”

Spread the love

Daga | Ahmad Aminu Kado,

Zaɓaɓɓen Councilon Gyellesu Ward, zaria city, Kaduna state, Hon Aminu Sani Minister ya zama shugaban wata ƙungiya dake kishin al-ummar Jihar Kaduna mai suna “ZA’BIN ALLAH SHINE ZA”BIN MALAM, ZA”BIN MALAM SHINE ZA”BIN AL-UMMAR JIHAR KADUNA” wadda aka ƙirƙira kwanan nan tare da tarin manufufi dake cikin ta na ganin makomar Al-ummar Jihar Kaduna a zaɓe mai gabatuwa na

Kungiyar “ZA”BIN ALLAH SHINE ZA”BIN MALAM” ta yanke hukuncin bawa Hon Aminu Sani Minister shugaban cin ƙungiyar ne duba da yadda ta ga ya ƙware wajan taimakon Al-ummah, kuma shine a ran shi, tare da taimaka masu ta fanni daban-daban a fadin Jihar Kaduna musamman yankin da yake wakilta na Gyellesu Ward dama Zaria baki ɗaya, shine suka yanke hukunci bashi janragamar ta domin faɗuwa tazo daidai da zama…

Wannan ƙungiya manufofin ta sune, sun ƙirƙiro tane domin biyayya ga Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’i, kuma sun tabbatar da cewa duk abunda Gwamna zai zaɓa masu a matsayin wanda zai gajeshi, domin sun tabbatar da cewa ba zai zaɓa masu mara kishin Al-ummah ba, saboda shiyasan wanda zai kare martaba da mutuncin Al-ummar Jihar Kaduna baki ɗaya, kuma su masu biyayyane, sanadiyyar kafa kungiyar kenan kuma sharuɗɗan ta kenan…

Bugu da ƙari ƙungiyar ta cigaba da cewa saboda Maigirma Gwamna ya kawo cigaba a Jihar ta Kaduna wanda tunda aka kafata ba’a taɓa kawowa ba, kuma sun tabbatar da cewa Maigirma Gwamna Malam Nasiru shine ya ke da hurumin yaga waye ya dace tare da cancantar gadar shi a zaɓe mai zuwa wanda zai cigaba da aiwatar da waɗannan abubuwa na cigaban Al-ummah, shiyasa wannan ƙungiya take biyayya a gare shi akan cewa duk abunda Allah ya zaɓa to shine Maigirma Gwamna zai zaɓa kuma shine Al-ummar Jihar Kaduna zasubi da yardar Allah…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button