Zaɓen 2023: Hotunan yaƙin neman zaɓen shugabancin Najeriya mai ɗauke da fuskar Saraki ya cika titunan Abuja maƙil.

An wayi gari da ganin hotuna masu ɗauke da taken “Bukola Saraki domin zaman shugaban ƙasa 2023” a lungu da saƙon babban birnin tarayya, wato Abuja.

Fastocin da aka gani maƙil a cikin garin Abuja

Pastocin da aka saka dai, angansu ne ɗauke da hotan tsohon shugaban majalisar dattawanne ɗauke da wani rubutu da aka yi shi da yaren nasara watau “Reset Nigeria 2023” ma’ana “Sake saita Najeriya a shekarar 2023”

Saraki a lokacin da yake shugaban majalisar dattawan Najeriya

Idan za’a iya tunawa, Saraki tsohon ɗan majalisa ne daya jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar hamayya ta PDP, sannan kuma yanzu haka shine shugaban kwamitin sasanta yan jam’iyyar PDP tare da fito da dabarun yaƙin neman zaɓe.

Bukola Saraki da Bature

Bugu da ƙari, zaɓen 2015, Saraki ya haɗu da manya manyan jiga jigai na siyasa domin kafa jam’iyyar APC, amma fa ya sake dawowa jam’iyyar PDP ne kafin zaɓen shekarar 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *