Siyasa

ZAƁEN 2023: Kungiyar fulani Miyetti Allah keutal Hore da Kungiyar Manoma sun bayyana goyon bayan su ga Bola Tinubu.

Spread the love

Manoman Arewa da makiyaya Fulani a ranar Litinin din da ta gabata sun yi alkawarin marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu goyon baya, a wani taro da suka yi a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar jam’iyyar APC ya yi alkawarin gudanar da gyare-gyare a fannin noma, kamun kifi da kiwo wanda zai sa masana’antar ta yi fice

Jami’in yada labarai na Tinubu, Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Tinubu ya kuma yi alkawarin sanya fannin noma ya zama tubalin tattalin arzikin Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Daga cikin kungiyoyin da suka amince da tsohon gwamnan na jihar Legas sun hada da kungiyar manoma ta Najeriya, Miyetti Allah Keutal Hore, kungiyar masara ta Najeriya, kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya da kuma kungiyar masu sana’ar noma ta Najeriya.

A tsakiyar shirin, Tinubu ya nada shugaban kungiyar gwamnonin ci gaba kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, da ya jagoranci wani kwamiti da zai tsara wani tsari da zai taimaka wajen sanya bangaren noma ya mamaye matsayin da ya dace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button