Siyasa

ZABEN 2023: Atiku ya shiga matsalar bayan Jiga-jigan Kwamitin Yakin Neman zaben sa sun kaurace masa.

Spread the love

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku/Okowa (PCC), reshen jihar Imo, ya koka kan yadda jiga jigan Kwamitin sukayi watsi da kamfen din na Atiku.

Daraktan Hukumar PCC na Jiha, Hon. Greg Egu, tare da wasu membobi, ya daga murya a yau ranar Alhamis, a wani taron manema labarai a Owerri.

Kwamitin na PCC ya ce wadanda aka zaba na tsohon gwamnan jihar, Rt. Hon. Emeka Ihedioha, ya kasa halartar tarukan kwamitin uku da suka gabata.

Hon. Egu ya bayyana cewa kiraye-kirayen da jam’iyyar ta yi na hada kai domin ganin Atiku/Okowa ya samu nasara a jihar ya ci tura.

Ya gabatar da cewa shugaban jam’iyyar na jihar, Cif Charles Ugwu shi ma ya karkata ga kwamitin.

Daraktan ya yi kira ga sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ta sa baki cikin lamarin.

Sai dai ya ci gaba da cewa kwamitin na aiki ba dare ba rana domin ganin an samu nasarar yakin neman zaben.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button