Zaben Edo:- Shugaba Buhari Ya Ganawar Sirri Da Ganduje Da Mai mala Buni.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yau Litinin, ya karbi bakuncin Shugaban Kwamitin Rikon kwarya na jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni Na Yobe, da gwamnan jihar Kano, Abdulahi Ganduje, a fadar gwamnati a Abuja.

Duk da cewa Shugaban kasar ya gana da gwamnonin biyu bayan sun kulle kofa, kuma maziyartan ba su yi magana da ‘yan jarida ba, ana zargin sun gana ne a kan sakamakon zaben gwamnan na Edo a karshen makon da ya gabata.

JARIDAR DAILY NIGERIAN ta rawaito, cewa dan takarar APCa kujerar gwamnan jihar Edo, Osagie Ize-Iyamu, ya sha kaye a hannun gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Godwin Obaseki.

Ganduje, wanda shi ne Shugaban Kamfen din yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo na jam’iyyar APC, da takwaransa na Jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda shi ma dan majalisar ne, sun shafe karshen mako a garin Benin domin jiran yin Nasara a kujerar Gwamnan Jihar, sai dai hakan bata samu ba garesu.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.