Zaben Kananan Hukumomi a Kano;- Jam’iyyar PDP Ta shiga Rudani.

A jiya Talata ne Jam’iyyar PDP reshen jihar kano ta Sanarda Janyewa daga takarar Shugabancin kananan hukumomi da za’a yi a ranar 16-01-2021,

Sanarwar da shugaban jam’iyyar rikon kwarya a Jihar Hon. Dr. Danladi Umar Abdulhameed tambarin kagara, ya sanyawa hannu.

Sanarwar tace “mun janye takarar domin Gwamnatin jihar ta shiya magudi a zaben kamar yadda akayi mana magudi a zaben Gwamnan jihar a shekarar da tagabata Inji sanarwar.

A yau laraba kuma sai ga wata sanarwa da Jam’iyyar ta fitar dake nuna cewar Jam’iyyar tana cikin masu yin zabe, basu janye ba, wannan sanarwar tana dauke da sa hannun Muhammina B. Lamido, wanda ya nuna cewa shine Shugaban Jam’iyyar PDP reshen karamar Hukumar Dala ta Jihar Kano.

Sai dai Jaridar Mikiya da ta Tuntubi Shugaban Jam’iyyar PDP, a jihar kano ta wayar tarho, cewa yayi. Wannan Sanarwar Karyace PDP ta janye daga wannan zaben domin babu Adalci a ciki.

Tambarin kagara, ya zargi wannan Sanarwa ta fitone daga bangaren Aminu wali, wanda ke yiwa Jam’iyyar PDP zagon kasa a Kano.

Yace Janyewar da PDP tayi daga wannan zaben bai yiwa Bangaren APC dadiba shi yasa suke so suyi, Amfani da wannan damar domin rudar Mutane.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.