Siyasa

ZABEN2023: Insha Allahu Uba sani shine Gwamnan jihar Kaduna na gaba ~Cewar Gwamna El rufa’i.

Spread the love

Gwamna Mallam Nasir Ahmed El-rufai ya bayyana hakan ne a makon daya gabata a lokacin da yake gabatar da ma’aikatan ofishi ga sabon Esu Chikun, Mai Martaba Isyaku Yari. Gwamnan ya jinjinawa Sanata Uba Sani, ya bayyana shi a matsayin jakada mai aminci, mai rikon amana kuma wanda ya cancanta da zai ci gaba da kawo sauyi da gwamnatinsa ta fara a farko.

Malam Nasiru EL’rufa’i Yana Mai cewa a zaben 2023 ya Zama wajibi ku zabi Wanda zai cigaba da Ayyukan da muka faro mutun Mai nagarta Kuma shine Uba sani ya Kuma bayyana cewa Yana da jama’a su zabi Mohammad sani dattijo amatsayin Sanatan Kaduna ta tsakiya.

A Karshe Gwamna ya gabatar wa da Sarkin Sanata Uba sani Yana Mai cewa Mai martaba ga Sanata Uba sani Kuma Gwamnan jihar Kaduna na gaba insha Allah.

Sanata Uba sani yanzu Haka shine Dan takarar neman Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar APC Kuma Dan takara mafi karfi ta hanyar samun karbuwa daga talakawan Jihar ta Kaduna.

Ana yabon Sanata a fannin kawo cigaban ga al’ummar jihar ta Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button