Siyasa

Zamu fara Kiran sunayen munafukai a cikin tafiyarmu ta APC A jihar Kano Kuma ba zamu kyale su ~Cewar Gawuna.

Spread the love

Mataimakin Gwamnan jihar Kano Kuma Dan takarar Gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyar APC ya ce yanzu ba zasu sake lamuntar munafurcin munafukai ba a tafiyar su Dan takarar Gwamnan ya bayyana hakan a wani Zama na masu ruwa da tsaki wanda Gwamna Ganduje ya jagoranta a gidan Gwamnatin jihar.

A wani faifain murya da freedom ta wallafa an jiwo muryar Gawuna Yana cewa Ina rokon masu ruwa da tsaki su kauracewa tunanin samun ku’di daga gareshi domin idan sukayi hakuri wannan Gwamnatin tasu Bayan sun lashe zabe ya Kuma cewa shi Allah ba a wasa dashi Kuma Wanda zaiyi wasa da allah shi Allah zai rabu dashi mu daina wasa da allah a maganar nan ta annamimanci nasha yinta Amma haryanzu ba a daina Mai girma Gwamna zai Kai Lokacin da zamu fara Kiran sunan Mutane Muna Gaya masu wallahi ba za ayi wannan damu ba duk mutumin da zai cigaba da annamimanci yazo Nan yace kaza yaje can yace kaza koya fara shirya Abu tunma abin bai zo ba wallahi Mai girma Gwamna zamu Gaya maka Kuma zamu fara Kiran suna mu fa’di su wane da wane haryanzu Basu daina ba.

Wannan annamimancin shine yake jawo duk abinda yake faruwa inji Gawuna.

Maganar ta Gawuna ta biwo baya ne Bayan kwanaki daya da Gwamnan jihar Kano ya sasanta rikicin Hon Alhassan Ado doguwa da Murtala sulen garo.

Jam’iyar APC na fuskantar baraza a hannun abokan hamayya a jihar ta Kano musamman jam’iyar NNPP Mai kayan marmari ta Sanata Rabi’u musa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button