Siyasa

Zan azurta mutune miliyan 20 nan da 2030 ta hanyar mayar dasu miloniyoyi idan aka zabe ni shugaban kasa – Yahaya Bello.

Spread the love

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023, gwamnatinsa za ta samar da attajirai miliyan 20 a shekarar 2030.

Gwamnan, a ranar Asabar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

Gwamnan ya bayyana aniyar sa ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin wani taro a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Bello ya kara da cewa idan har ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi nasara.

“A shekarar 2018, da APC a sirdi, adadin ya ragu zuwa kusan mutane miliyan 87, amma duk da haka Najeriya ta wuce Indiya a matsayin hedikwatar talauci a duniya,” in ji shi.

“A cikin wannan watan ne Najeriya ta hanyar kokarin shugaban kasar ta bar kasar Indiya, ta kuma rage adadin zuwa mutane kusan miliyan 70.

“Don haka a bayyane yake cewa hanyarmu ta samun ci gaban kasa ta ta’allaka ne wajen fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci.

“Gwamnatin Buhari tana da burin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.

“Yahaya Bello zai yi karin kudirin samar da milobiyoyi miliyan 20 nan da wannan shekara ta 2030 da nufin kowanen su zai ba wa wasu ‘yan kasa biyar damar.”

Hafsat Abiola-Costello, diyar marigayi MKO Abiola, ita ce babbar darakta a kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na Yahaya Bello.

Sanata Jonathan Silas Zwingina shi ne kodineta na kasa kuma shugaban yakin neman zaben shugaban kasa yayin da Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, mataimakin kodineta na kasa kuma mataimakin shugaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button