Siyasa

Zan dora daga inda Malam El rufa’i ya tsaya idan na zama Gwamnan jihar kaduna ~Cewar Sanata Uba sani

Spread the love

Sanata Uba sani ya bayyana Hakan ne A yau ranar Talata a lokacin da yake kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan jihar kaduna Sanatan yace yau Jihar Kaduna ta tsaya cak a daidai lokacin da na bayyana aniyata ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023.

A jawabin sa a wajen sanarwar da aka gudanar a Sakatariyar Jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna yi alkawarin dorawa tare da gina kyakkyawan gadon Mulkin sarautar Gwamna mara gajiyawa, mai Samar da kirkire-kirkire da wadata, wanda ba ya misaltuwa, Malam Nasir El-Rufai. Mallam El-Rufai ya canza fasalin jihar Kaduna. Ya sake fasalin mulki ta hanyar samar da ababen more rayuwa da ba a taba ganin irinsa ba da magance kalubalen ci gaban jihar. Ya daga darajar shugabancin jihar inji Sanatan.

Sanatan ya Kara da cewa El rufa’i babban mai imani ne akan falsafar mulki Na karanta shi tsawon shekaru da yawa. Zan tsayawa a bisa kyakykyawan matsayi na dorewa ga shimfida iyakoki na kyakkyawan shugabanci a wannan jiha tamu mai albarka. Na kasance mai nasara. Na nuna hakan a Majalisar Dokoki ta Kasa. Ina mai kishin jin dadi da ci gaban al’ummar jihar Kaduna. Da sanarwa a yau na kulla yarjejeniya da daukacin al’ummar jiharmu mai ma’ana da albarka da Girmamawa.

Daga Karshe Sanatan ya mika godiyarsa ga jama’a magoyansa Inda ya ce Ina nuna godiya ga Shuwagabannin kananan Hukumomi na babbar jam’iyyar mu, ‘yan majalisar jiha da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka yi tafiya tare da ni zuwa sakatariyar jam’iyyar ta jiha domin gabatar da shela ta, a cikin farin ciki da magoya bayan jam’iyyar da ‘yan jihar Kaduna suka yi. A bisa gagarumin aikin da shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar Kaduna da shugabannin kananan hukumomin APC suka yi, na ba su gudummuwar motoci guda 59 don taimaka musu wajen saukaka ayyukansu da kuma zaburar da su don tunkarar yakin zabe na 2023.

Ina kira ga al’ummar jihar Kaduna da daukacin magoya bayanmu da masu fatan alheri da su zo tare da ni a wannan tafiya ta hadin gwiwa. Iko naka ne. Zan zama bawanka. Zan baku kyakkyawan sakamako Za mu yi hadin gwiwa a kan manyan ayyuka na Gwamna El-Rufa’i. A Yayin da muke kokarin bude sabbin kofofi Muna addu’a Allah Madaukakin Sarki ne zai zama jagora da garkuwarmu. A gare shi ne ƙarfinmu yake.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button