Siyasa

Zan Kaura Daga Kaduna Bayan mika mulki – El-Rufai

Spread the love

Gwamna Nasir El Rufa’i ya yi alkawarin kaura daga jihar Kaduna a ranar 29 ga Mayu, 2023, bayan ya mika wa wanda zai gaje shi, domin kada ya tsoma baki cikin gwamnatin da ke tafe.

Ya kuma ce ba zai karbi bukatu daga mutanen da ke neman ya ba su takardan magajinsa ba ko kuma ya tsoma baki a harkokin tafiyar da gwamnatin APC mai zuwa.

Gwamnan wanda ya yi magana a wani taro na garin da shiyyar sa ta tsakiya ta shirya, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Sanata Uba Sani ne zai gaje shi.

Ya kara da cewa ya san dan takarar APC sama da shekaru 20 kuma ya tabbatar da kwazonsa a siyasance.

El Rufa’i ya ce Gwamna mai zuwa Allah zai yi masa jagora idan ya na da zuciya mai tsarki, Sanata Uba Sani mutum ne nagari wanda kuma zai yi nagartaccen gwamna.

Ya bayyana Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya cancanta wanda zai kai jihar Kaduna matsayi mafi girma idan aka zabe shi a matsayin gwamna.

Bugu da kari, ya shawarci al’ummar jihar Kaduna da kada su cika masa bukatuwa Uba Sani, a ba shi mukamai ko kwangila idan ya zama gwamna.

Da yake jawabi a wajen taron, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa ya kasance dalibin makarantar gwamnati da manufofin Malam Nasir El Rufa’i tsawon shekaru 20 da suka gabata kuma ya samu ‘digiri’ da dama a dalilin haka.

“A wannan makarantar, akwai wasu da suka shiga gabana, irin su Sakataren Gwamnatin Jiha, Malam Balarabe Abbas Lawal, wanda shi ne babba na. Koyaya, makarantar ba ta da ranar kammala karatun. Don haka har yanzu muna koyo,” inji shi.

Sanatan wanda ya yi alkawarin ci gaba da tsare-tsare na gwamnatin El Rufa’i, ya yaba wa gwamnan kan sake farfado da harkokin mulki a jihar Kaduna.

“Kafin zuwan wannan gwamnati, ana raba dukiyar gwamnati a tsakanin wasu ’yan jiga-jigan, bayan biyan albashi. Don haka babu abin da ya rage na ci gaba, duk da dimbin albarkatun da jihar Kaduna ke karba a matsayin kason tarayya.

“Amma Malam Nasir El Rufa’i ya canza wannan labari ta hanyar inganta ilimi, inganta harkokin kiwon lafiya da gina ababen more rayuwa da ke amfanar mutanen jihar Kaduna nagari, maimakon wasu tsirarun mutane,” in ji shi.

Dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC ya bayyana cewa sakamakon dimbin jarin da aka zuba a fannin ilimi ya fara yin tasiri domin jihar Kaduna ita ce jiha ta hudu a kasar da dalibanta suka samu maki biyar da suka hada da Ingilishi da lissafi a jarabawar manyan makarantun sakandare.

Sani wanda ya ce gwamnati ba za ta iya biyan kudaden ilimi kadai ba, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su dauki nauyin karatun manyan makarantu masu albarka amma ga marasa galihu.

A cewarsa, a kwanakin baya ya baiwa dalibai 280 tallafin karatu a manyan makarantun jihar Kaduna domin su ci gaba da karatunsu.

Sanatan ya kuma ce gwamna El Rufa’i ya baiwa ‘yan kasuwa karfin gwiwa, ta hanyar kafa tsarin jinginar gidaje inda za su biya kashi-kashi don mallakar shaguna.

Ya tuna cewa a baya an ware shaguna ga manyan jami’an gwamnati da jiga-jigan jam’iyya, a matsayin wata hanya ta taimakon jama’a, inda su kuma suke ba da su ga ‘yan kasuwa a kan farashi mai sauki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button