Siyasa

ZAURA: Amsoshin Da Ba Fahimta Ba Game Da Manyan Nasarorinsa

Spread the love

Siyasa hanya ce ta samun saƙo cikin sauƙi zuwa kan madafun iko, wannan kuma ƙila shi ne ya ja hankalin al’umma daban-daban masu mabambantan dalilai, muradi, mafarki da ƙudiri.

Kowa da kowa da ƙudirinsa na nema a cikin waɗannan rabe-rabe a siyasa. Saura su kan kalle ta a matsayin hanyar yi wa jama’ar yankinsu hidima inda su ke komawa neman haɗin kai da goyon bayan jama’arsu domin cimma wannan buri. Wasu kuma su kan kalle ta a matsayin hanyar azurta kansu ta hanyar wadaƙa da dukiyar al’umma. Sun ɗauke ta a matsayin hanyar zuba jari a samu riba”.

Mu mance da duk wannan gaba ɗaya, al’ummarmu sun yi dace da samun nagartattun mutane waɗanda su ke da kykkyawar manufa da kykkyawan ƙudiri da buri gami da muradi mai kyau na yi wa al’ummarsu hidima kamar yadda na bayyana a sama. A kodayaushe mu na murna da namu, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim (A.A Zaura), wanda ya ke sahun gaba a cikin layin mutanen da su ka ɗauki siyasa da manufa mai kyau….

Da dama daga cikin ire-iren waɗannan mutane su na nan a loko da saƙo na wannan ƙasa, waɗanda an gani an ba su amanar dukiyar al’umma sun tafikar yadda ya kamata. Wasu kuma waɗanda ba sa cikin fagen siyasa su na da wannan nagarta waɗanda sun cancanta a shigo da su fagen siyasa batare da bambancin addini, yare, ƙabila ko sauran bambamce-bambance marasa alfanu ba. A kawar da bambanci ko son kai a zaɓi mutane waɗanda za su ceto mu daga masifun da mu ke ciki a wannan ƙasa..

Mutane da halinsa, waɗanda su ke ƙonewa ba gaira ba dalili su shiga halin yunwa wajen ba da mamaki su ɗaukaka matsayin al’ummarsu da barin kykkyawar gobe su na da ƙarfin hali na jure duk wani yarfai, da keta alfarma da gurguwar fahimta waɗanda wawaye su ke yi musu. Daɗi da ƙari, akwai mutanen da duk runtsi duk wuya ba sa karaya su na cigaba zuwa cimma mafarkinsu ba tare da ɓuya ba.

A cikin mutanen da ke da muradin samun kujerar zama gwamna waɗanda al’umma su ka aminta da himmarsu akai, A.A Zaura shi kaɗai ya ke da shaidar bai taɓa riƙe wani matsayi a gwamnati ba na zaɓe ko na naɗi. Mutum mai hankali babban ɗan kasuwa, babu wani wanda zai ƙalubalance shi da almobazzaranci da dukiyar al’umma domin bai taɓa riƙe kowane matsayi ba. Kusan duk masu neman wannan matsayi tare da shi, sun taɓa riƙe muƙamai na siyasa na zaɓe ko naɗi, wasu ma har yanzu su na kai amma banda wannan matashi, shi kaɗai ne bai taɓa ba. Ya sha gaban saura akan wannan batu, babu wani zargin rashawa a kansa, ko zargin karkatar da dukiyar al’umma. Akan wannan gaɓa shi ne sama da sauran.

A lokacin da ya bayyana shigarsa cikin jam’iyyar APC a hukumance, masu biye da ni sun karanta rubutuna mai taken: A.A Zaura: Mikiya Ta Sauka”. Inda na nuna zuwan babban kifi wanda bai zo don ya shiga cikin adadi ba, sai domin ya yi tasiri cikin shimma da ƙwazo da kykkyawan buri na ɗaga martabar jam’iyyar cikin fafatukar neman wannan kujera. Mutane da dama sun faɗi game da hasashena domin sun yi tunanin ya zama ɗan jam’iyya kawai, sannan ba shi da ƙarfin da zai iya neman wannan kujera. Sai dai a yanzu sun shaida da kansu labarin ya sha bamban duba da abin da su ke gani. Ya shimmatu kan abubuwan da ba kowane ya yi tunanin zai yi ba. Matashin ɗan siyasar ya ɗauki matakin tsakiya zan faɗi wannan batare da wata fargaba ba. Ba ƴan kaɗan ne su ke kallonsa akan hanyar zuwa gidan gwamnati 2023 ba.

Ya ɗaukaka, a kullum karɓuwa ya ke samu daga al’ummar Jihar wanda hakan ya ke hana sauran abokan nemansa barci. Salonsa na yin siyasa mai tsafta da ayyukan jin ƙai da temakon al’umma tun daga tushe da babban tallafi na bunƙasa rayuwarsu daga dukiyarsa, ba shakka ba shi da na biyu. Ba tare da bayyana shaƙuwarsa ta taimako da ɗaga darajar makarantun Islamiyya da babban taimako ba, ya sha bamban da sauran ƴan siyasa. Matashin ɗan siyasar ya himmatu da ƙoƙarin tallafi ga al’umma mabuƙata da gina makarantu da ba ta tallafin kayan kiwon lafiya da ɗaukan nauyin jinyar al’umma, da ba da tallafin karatu, da raba jarin dogaro da kai, da raba tallafin kayan abinci da sauran ɗumbin ayyuka da dama da ban bayyana ba. Yanzu ya ɗaukaka ya tashi daga matsayin abin “so zuwa matsayin wanda aka fi so”. Tunawa da rubutuna da ya gabata mai taken: A.A. Zaura daga wanda ake so zuwa wanda aka fi so”.

Ba kokwanto mutumin, ya zama wanda aka fi ambato cikin ƴan siyasar Jihar, waɗanda su ke tsoro game da kasancewarsa cikin jam’iyyar a yanzu sun himmatu wajen yaɗa maganganu na ƙarya da ƙage domin ɓata shi a idon al’umma. Tunawa da rubutuna mai taken: “Komawar A.A Zaura Jam’iyyar APC, Abin Tsoron Dusashewar Tauraruwar Saura”.Ayyukansu sun tabbatar da hasashena kan wannan ƙwararren ɗan wasa da ba za a iya dakatar da shi ba.

Daɗi da ƙari mutane daga ciki da wajen Jihar a kullum tambayoyi su ke yi kala-kala game da wannan mutum na musamman a wannan lokaci. Kykkyawan fata ga ɗan takara, saboda zama cibiyar tattaunawa da nuna kulawa a tsakanin al’umma wata alama ce da ke nuni da yadda mutumin ya zama tauraro.

Abubuwa da dama ne su ka haifar da ta’azzarar waɗannan tambayoyi. Mutumin ya na himmar fidda maƙudan kuɗaɗe wajen kyautata rayuwar al’umma waɗanda ba a tsammani a yanayin siyasarmu. Banki ne da ya zama wajibi jama’a su yi tambaya. Ya na tafikar da komai cikin mutunci da martaba a yaƙin neman zaɓensa wanda ya barranta da hargitsi da ɓata suna da rusa abokan hamayya, wannan abin a yaba ne. Dattakonsa wajen tafikar da siyasa ya su na jan hankalin al’umma. Tare da haka gaba ɗaya, tawagar ayarin motocinsa waɗanda su ke mamaye da babbar mota jif SUV waɗanda ba ta jin harsashi waɗanda sun kai guda 20 su ma su kan zama abin tattaunawa. Wannan kaɗai kan jefa tambayoyi zukatan al’umma, a ya yin da wasu da dama kuma su na fassarori kala-kala da kammalawar ƙiyayya.

Farawa da, da dama su kan yi tambaya kan asalinsa da kuma ta ina ya zo ? Amsoshi can da can su na da faɗi a buɗe. An haifi Zaura a unguwar Dakata kuma anan ya girma. Ya yi karatun alqur’ani ya kuma haddace shi tun ya na ƙarami. Daga nan ya fara karatunsa na Firamare da sakandire a mahaifarsa Zaura. Yanzu haka ya da karatun digirin digirgir wanda ya yi a babbar jami’a ta Baze wanda kuma shi ne ya zama zakara da ke jan ragamar sauran ɗalibai tsangayar karatunsu gaba ɗaya. Ɗalibi ne mai ƙarfin basira da kykkyawar ƙwaƙwalwa.

Wasu kuma kan yi mamakin ya aka yi ya tara dukiya haka batare da ya taɓa riƙe matsayi a gwamnati ba, sannan kuma ba shi da wani shagon kasuwanci a duk faɗin Jihohi. Bayani a warware, A.A Zaura babban ɗan kasuwa ne na duniya wanda ya ke da kamfanoni a gida da ƙasashen waje. Ya na da ƙulli da alaƙa da manyan ƴan kasuwa masu ƙarfi na duniya. Sannan wannan zamanin fasahar wanda mutum zai samu kuɗaɗe ta hanyar gudanar da kasuwancin biliyoyin Naira Online ya na zaune a ɗakinsa idan ya ga dama, a fahimci A.A Zaura ɗan kasuwa ne da ke tafikar da manyan kamfanoni a duniya da cikin gida Nageriya.

Sannan wani taimakon Allah, Zaura ya samu albarkar dace da tunanin kasuwanci mai kyau da zuciya ta musamman. Kyauta ce daga Allah wanda ya ke taimakawa waɗanda ya so cikin bayinsa batare da wani ƙalubale ba. Abokan kasuwancinsa gaba ɗaya sanannu ne, waɗanda su ke kasuwanci mai nagarta, ana lissafa su a cikin manyan ƴan kasuwa na duniya. Gwamnanmu da zai zama, ya na rayuwa a kewayensu, ya na tafikarwa cikin tsafta, da samun damar mallar kamfanoni a gida da waje

Mutane kan yi mamaki wai mai ya sa ɗan takarar ya ke cigaba da yaƙin neman zaɓe da yaɗa mafarkinsa na neman zama gwamna duk kuwa da cewar gwamnan Jihar da manyan ƴan siyasar Jihar masu ƙarfin faɗa aji ba su nuna wanda zai gaji gwamna mai ci ba. Zargin da zai zama abin watsi saboda babu wani bayani daga gwamna ko kwamishinan yaɗa labarai. Mutumin ba shi da kunnuwan da zai cigaba da sauraren waɗannan maganganu na ƙarya da zarge-zarge marasa tushe da makama. Wani zai iya cewa zai ruɓunya ƙoƙarinsa da ɗaga yaƙin neman zaɓensa zuwa babba mataki. Mutum mai biyayya ta haƙiƙa ga gwamna Ganduje ya na bayyana soyayya ta gaske cikin tsari batare da zaƙewa ba. Shi ɗin mayaƙi ne wanda ya ke cikin siyasa domin shawo kanta ba wai shawo kai ba. Mutum ne mai ƙarfin zuciya.

Wasu kuma kan yi tuhumar ta yaya matashin ɗan siyasa ya ke karɓan jirage masu zaman kansu a harkarsa. A.A Zaura mutum ne mai ƙarfin tattalin arziƙi, ya na matakin da zai iya mallakar jirgi mai zaman kansa in ya na so.

Sannan akwai shahararriyar jita-jita da ake yaɗawa cewa mutumin ya na aiki ne a ƙarƙashin babban hamshaƙin attajirin nan na ƙasar Amurka, ma’assasin kamfanin Microsoft, Bill Gates. A gaskiyar magana mutumin a tsaye ya ke da ƙafafunsa wanda dubban al’umma ne su ke aiki a ƙarƙashinsa a kamfanoninsa. Ba ya yi wa kowa aiki face kansa. Daɗi da ƙari mutumin ya na alaƙa da manyan ƴan kasuwa na duniya masu ƙarfin tattalin arziƙi irinsu Aliko Ɗangote da sauran ire-irensa.

Wasu kuma na tunanin Zaura yaron Tinumbu ne, shi ne ya turo shi ya nemi takarar abin dariya! Idan har wannan zargi gaskiya ne, wa ya turo shi ya nemi takarar a 2019 ? Wanda da kansa ya tsaya ya kuma ɗauki nauyin sabuwar jam’iyya da ake kira Green Party of Nigeria (GNP). Gaskiyar magana a buɗe ita ce, A.A Zaura ɗan kasuwa ne, kuma ya na da alaƙar siyasa da Jagaban sannan bai taɓa ɓoye goyon bayansa ga jagoran jam’iyyar APCn na ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ba.

A yanzu kowane ɗan Jiha mai ƙaunarta da son cigabanta ya zama lallai ya mara baya ga ayyukan A.A Zaura. Jihar ta yi dace da samun albarkar wannan mutumin mai nagarta da nasara wanda ya himmatu kan cigaban Jihar. Idan har ya kai ga nasara zai kare dukiyar al’umma, zai nusar da al’umma muhimmancin shugabanci nagari cikin gaskiya da adalci, sannan kuma zai buɗe ƙofa ga ƴan kasuwa na duniya masu zuba hannnun jari su shigo su kafa masana’antu a samarwa al’umma aikin yi.

DAGA Shariff Aminu Ahlan
Babban mayaƙin gwamna Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button